Yadda zaka hada website

Yadda zaka hada wapka website pasali na 1 
Jeka daya daga wadannan website din dan ka kirkiri naka
www.wapka.mobi
www.mywapblog.com
www.blogspot.com
www.xtgem.com
Idan kun shiga zaku ga SIGN UP saiku shiga nan ku cike duk abinda suka bukata.
Ita wapka sai kayi mata design irin wanda kakeso website dinka ta kasance,kana iya yi mata design wanda download din abubuwa kawai za'a rikayi,kuma kana iya
yin mai FORUM wanda zaka rika post,
i.e cheat,expo,news,advt,busineess.etc.
Nan gaba kadan zan fara koya yadda zakuyi design na WAPKA.
YADDA YA KAMATA SUNAN WEBSITE DINKA YA KAMATA YA KASANCE.
Kabin ka bude website ka tsaya kayi tunanin sunan da zaka sanya
mashi,wanda zai sami karbuwa ga jama'a.
Kuma karda ka sanya kalmomi da yawa, ka sanya kalmomi yan kadan masu sauki.
Misali
www.mousabbndaudalg.com
wannan sunan yayi yawa masu ziyarta zaiyi masu wuyar harda cewa amma idan ka sanya
mara yawa za'a fi saurin rikewa
misali www.ringiminian1.tk
MENENE AMFANI BUDE WEBSITE.
Bude Website yana da amfani sosai ga al'umma ta bangarori da dama domin ta
wannan hanyar ana amfanuwa da ilimi kala_kala.
Zaka iya bude site domin
*Kasuwanci
*Yada Addini
*Watsa Labarai
*Neman Kudi
*Nishadi
*Dadai sauran abubuwa.

Comments

Popular posts from this blog

Sunayen matan manzan Allah /yayansa/sahabbansa

Sakon soyayya daga budurwa zuwa saurayinta

Shin ko kasan menene soyayya