Yadda budurwa zatafin san hira da kai
![]() |
YADDA BUDURWARKA ZATAFI SON SHIRA DAKAI ACIKIN SAMARINTA
barkanku da warhaka masoya maza damata ,ga happy sallarku.
Na wasu yan dabarune da zasu sa budurwarka tafi son shira/fira dakai acikin samarinta.
Haqiqa shira tsakanin masoya abace meqara danqon soyayya nesa bakusaba sannan kuma ananne dukkan wasu bayanai ake samunsu tsakanin saurayi da budurwa tahanyar musanyar ra'ayi .A WASU LOKUTAN SAIKAJI SAURAYI YANA COMPLAIN WAI BUDURWARSA IN SUNA SHIRA HAR GYANGYADI TAKEYI TABARSHI YANA SURUTU. WANI KUMA KAJI TACEMASA BACCI TAKEJI ,WANIKUMA KAGJIA YACE YANAGANIN ALAMUN BATA SON SHIRAR DA SHI A WASU LOKU
TAN,KOKAJI WANI SUNA SHIRA AMMA DA WANI SAURAYI YAZO SAITATAFI TABARSHI A TSAYAE DAGA MINTI 2 SAIKAGA TA SHARE MINTI 40 TASHANYA SAURAYIN TANA NA FARKO HARKAGA ZARGI YASHIGA TSAKANI SAURAYI YANAGA KAMAR BATA SONSHINE. YAN UWANA SAMARI HAKANTASA ZAN DANYI BAYANI AKAN SHIRA/FIRA MATUQAR KABI WADANNAN HANYOYIN TO ZAKAZAMA KAI BUDURWARKA TAFI SHIRA DAKAI KUMA BATA BARINKA TAJE GUNWANI HARMA ZUMUDI TAKE Kazo,harma tsimanka take kazo,kuma bata gajiya daka tambayeta yaushe zandawo zakaji tasama rana kusa.
*1 dafarko dai yan samri kusani iya shira nada muhimmanci sosai ,sannankuma ba wai iya surutu ratata ba shine IYA firaba a a wasu tsare tsarene daki daki, iya fira naqara danqon soyayya rashin iya fira na rage danqon soyayya .KUMA INBAKA IYA HIRABA KOMAI SON DA BUDURWA TAKEMA TO AKWAI NAQASU ACIKI.
1* Dafarko dai yazamana kafin kaje gun masoyiyarka fira/hira ka tabbata kana cikin tsafta ta jiki data sutura. Hadeda kwalliya. Domin mace akoda yaushe tana buri taganta tsaye da saurayi me tsafta da kwalliya abun sha'awa acikin qawayanta hakan kan matuqar burgeta da qaramata aji acikin qawayenta DAN HAKA KAZAMA ME TSAFTA DA KWALLIYA SADDA ZAKAJE HIRA KODA BUDURWARKA TANA SONKA SOSAI TO KA QARA DA KWALLIYA.
BAKUMA SAI KAYA MAI TSADABA A A WLH DA KAYAN 300 MA YA ISA kai dai ka'iaya dressing zabar machin kala jara jiki bawai sai masu tsadaba.
2*IYA TSAIWA YAYIN FIRA:
shima yana da muhimmanci afira ka iyatsaiwa ko zama yayin dakuke hira, wato kazama kana canza yanayi na tsaiwarka yayin dakuke fira kada ka dogare qiqam tsawon awa ko muntuna a a kana dan canjawa ,wasu lokutan kana motsa hannayenka wasu lokutan kana ruqesu wasu lokutan kana amfani dasu wajen musulta abunda kakefada .yazamana dai kana dan action haKama in azaune kake kana dan canja zama dai dai musali dabada style ,
DALILI KUWA IN KANA FIRA DA BUDURWARKA TO ANA ANKARE DAKAI WATO QAWAYENTA KO QANNUNTA. wasu har tsokanar budurwarka zasunayi wato qawayenta kaji sunacewa haka saurayin wance yake TSAYAWA QIQAM KO HAKA YAKE ZAMA KINKIRIM ,hatta ita budurwa zatagaji tana ganinka akame qiqam kamar gunki amma kana dan canja yanayin zama da tsaiwa lokaci lokaci,hakan yafi.
3*KULA DA YANAYIN DA BUDURWARKA TAKE CIKI
yana da kaya kakula da halinda budurwarka take ciki shin baccine takeji,bata da lafiyane,ranta abace ne dukkan su yana da muhimmanci ka fuskancihaka dan haka dakazo fira sai kaga alamominnan ko tafadama sai kadubata ,in abun rarrashine sai ka rarrasheta ,inna nasihane da bata haquri sai kaimata hakan inna jajantawane saika jajantamata daganan kabata dama taje gida takwanta ko ta zauna batare da kacikata da surutaiba .
DALILI MATA KANSAMI KANSU A WASU LOKUTAN SUJI BASA SONKOMAI A RAYUWARSU HAR SHIRAMA kuma kodawaye. sabodahaka inkana lura da irin wadannan lokutan to mace bata qinzuwa gunka fira koda bata da lafiya dan tasan da tafadama zaka dubata kace tazo ta kwanta.
AMMA IN BAKA LURA BAKA BARINTA TATAFI TO ZAI WUYA TAFITO A IRINWANNAN YANAYIN KO AIKAWA KAYI TAZO .ZATACE KUCEMASA YAYI HAQURI bani da lafiya dan tasan zakaitaimata surutune bazaka qyaleta da wuriba.
4*KIYAYE DUKKAN KALAMAN DA ZASUSATA JIN KISHI,KOBATA MATA RAI A YAYIN FIRA.
musali ai kinga qawarki wance tana bugeni ,ko kinsan wacce tana da qoqari ,ko aiwancema da budurwa tace mundade sosai ,hakan nasataji badadi aranta zataji bata son hira dakai sosai dawani saurayin yazo zata je gunsa tamanta dakai.ko taqi futowa dawuri .
5*ZABAR KALAMAI MASU DADI DA FARANTA RAI YAYIN FIRA.
Anaso kana amfani da zababbun kalamai masu faranta rai ga masoyiya,danhaka kazamana kana shirya kalamanka dakidaki
6* KYAUTATA SUNAN MASOYIYA YAYIN FIRA .
MUSALI
hafsana kinsan kaza da kaza,GIMBIYANA KAZA DA KAZA, to meya tawan? Abar alfaharina, etc
7*YAWAITA MURMUSHI GA MASOYIYA A INDA MURMUSHI YADACE,YAYIN FIRA.
yawaita murmushi abune me qara danqon soyayya ,lokutan da akafi son yin murmushi ga budurwa sune.
Farkon haduwarku a ranar wato ka aika akirata tafito yayin kallon fari da zakuhada ido da ita anaso kayimata murmushi mai sace zuciya sai yayin da kuka hada ido, ko kana bata amsa tana kallonka da yayin furtamata kalaman qauna da shauransu.
8* SATAR KALLO GA MASOYIYA YAYIN FIRA.
Shima na qara danqon soyayya ga abar qauna MUSAMMAN MA QARAMAR BUDURWA YAR 15 ZUWA 17. shi satar kallo masoyiya bata sanin sadda kafara sai dai kawai ta juyo kanta ko ta ankara taga kana kallonta.
Akwai shaura ajira
Ni ban iya firar bane da mungama gaisawa wani lokacin sai narasa me zanfada
ReplyDelete