Sakon soyayya

Aikawa da masoyiyarka wannan saqon.

Amincin Allah ya tabbata agare ki saurauniyar wannan zamani me haskaka duniyar masoya,masoyinki 
ya wayi gari cike da tunaninki idanuwan sa cika da kewarki,
kyawawan dabi'unki da
Ruqo da addininki na tabbatarmin bazanyi nadama a soyayyarki ba, salo da halayenki sune jigon farko na hadassa soyayyarmu hafsat inasonki ,inaqaunarki.

tabbaz hafsat kece burin raina .matuqar kifi bai dena son ruwa tabbas Hafsat  baranar da za tazo najuyamiki baya. 
Matukar sarrafaffun kalamanki nacigaba da sauka a kunuwana

Hafsat dazarar idanuwana sunyi duba izuwa madai-daiciyar fuskarki me cike da kyau da kwarjini nantake kyan fuskarki kan dimautani nantake nakan tsinduma cikin begenki da shauqin soyayyarki dazarar kin kalleni hade da murmushi me bayyana hasken fuskarki nantake,nakanji wani sinadarin farin ci medauke da sanyayyiyar iska me ratsa zuciyar ya lullubemin zuciya, musamman ma inzuciyata taharararo danni kadai Hafsat tafurta kalamannan yabawa nantake sai dikkan wata dimuwa tayi gaggawar ficewa hasken soyayya yabayyana ,lallai nayi dace da samu masoyiya tagari Hafsat soyayyarki itace farincikin raina,farin cikin raina kuwa cikar burina ,cikar burina kuwa na mallakeki hafsat.

Comments

Popular posts from this blog

Sunayen matan manzan Allah /yayansa/sahabbansa

Sakon soyayya daga budurwa zuwa saurayinta

Shin ko kasan menene soyayya