KO KASAN?
KO KASAN?
©Khadija S Muhd
*1.Ko* *kasan?* *kalamai masu dadi na sace zuciyar mace*
*2.Ko kasan? Namiji dan gaye yakan tafi da zuciyar kowacce irin mace duk isarta.?*
*3.Ko kasan? Tsafta a gurin Namiji wani abu ne da yake karamasa kima a idon mace?*
*4. Ko kasan? Namiji mai zafin kishi baya burge mata?*
*5.ko kasan? Namiji me yawan korafi, Mace na tsanar zama dashi?*
*6. Ko kasan? Mata basason Namiji me bin diddigi? komai sai yabi diddigin yanda aka yi shi, misali ya bada 10 kudin cefane, to idan ya dawo sai ya tambayi me kika siya.*
*7. Ko Kasan? Namijin dake sanya kansa cikin harkokin mata baya burge Mace?*
*8.Ko kasan? Namiji mai mammako ko kadan baya burge mata?*
*9.Ko kasan? Namiji mai zargi Mata gudunsa suke?.* *10.Namiji me saurin fushi ko fada, shima mata basa son shi.*
*11. Namijin da bai iya tsara magana ba, kawai kome yazo bakinshi sai ya sake yaraf. Sam bakin ba control.*
*12. Namiji me da baya damuwa da abinda ya shafi matarshi, shi kawai damuwarshi ita ce damuwa, damuwar matarshi kuwa shirme ce.*
*13. Namiji da inyi kwalliya yake kai kwalliyar ta shi waje, in dai kaga ya yi kwalliya to waje ya nufa.*
*14. Namijin da yake dadewa 'fira a waje, baya dawowa gida sai dare ya yi, lkcn kowa ya yi bacci , a lkcnne 'zai tada matar ta kawo mai abinci ta yi mai ka za tayi mai ka za alhalin tana 'cikin baccinta, akwai rashin adalci aciki.*
*15.Namijin da ke fifita aikinshi ko sana'arshi akan iyalan shi, duk abinda ya shafi sana'arshi to Allah Allah yake yaga ya yi, amma idan ya shafi gidanshi sai ya rika ma abun rikon sa kainar kashi..*
*16.Namijin da baya zama cikin iyalanshi ayi fira, yaji matsalarsu. Kullum sai yawo sai kace rakumi.*
*17. Namijin da baya sakin fuska acikin iyalanshi, duk ranar da aka ga dariyarshi to wani abu yake bukata ajikin matar ko kuma awaje ne.*
*18. Kazamin namiji wanda tsafta bata dameshi ba, yaje ya gama fankan fankan dinshi a kasuwa ya zo ya kwanta haka ba tare da yayi wanka yayi brush,yasa turare ba gashinan dai dagajaja.*
*19. Namijin da bai iya yabo ba, bai san idan ya ji me dadi ya yaba ba, sai dai ya yi shiru, amma duk randa akayi mara dadi har makota sai sun ji.*
*20. Namijin da baya nuna tausayi akan matarshi, tun ba idan tana da ciki ba, lkcn da abubuwa ke yi mata wahala. Sai yay ta hadata da aikin da zata wahala ko kuma idan ba tayi ba ya hauta da fada.*
Comments
Post a Comment