HANYOYI GOMA DA ZA A MAGANCE RADADIN SOYAYYA

HANYOYI GOMA  DAZA'A MAGANCE RADADIN SOYAYYA


Abinda da zai zo zukatan mutane shine ya ‘dan adam zai magance abinda bashi da iko dashi? Abin da lokacin da zai shiga zuciya baya shawara? Katsahan soyayya kan iya mamaya tayaya zaka sami kwanjin tantance ta? Soyayyar da bata bar masani ba duk da saninsa, bata bar jahili ba. Ba taga babba, bata kyale yaro ba. Duk wanda ta gitta ta gaban sa tana iya cin sa yaki.
E,nima nasan da haka, to amma bahaushe yace, “In hankali ya bata, hankali ke samo shi,kuma rigakafi yafi magani.”
Ga wasu matakai dan rage kaifin makauniyar soyayya.

1- ADDU’A
Addu’a babban makami ce ta hana fadawa kan dukkan mummunar kaddara. Bakin mu ya saba da fadin neman zabi na alkhairi wajen Ubangiji. Duk lokacin da aka hadu da abin so, a matsa da neman alkhairi a cikin haduwar.


2- TSORON ALLAH
Son gaskiya shine son da ake sa Allah cikin sa. Duk lokacin da shedan yayi galaba ido ya rufe kan so, to fa an sami matsala.


3- TARBIYYAR IYAYE
Tarbiyyar iyaye da nunawa yara illar dake tattare da damka wa zuciya yarda da amana da sakin jiki da ‘ya’ya da hira dasu dasa ido kan shige da ficen su nada tasiri kwarai kan dakushe kaifin aukawar su cikin makauniyar soyayya. Iyaye kada su yarda suyi nesa da yaran su ko zuciya koda sunyi nisa a zahiri tayi musu addu’a da basu shawara da nasiha.


4- SON GASKIYA
Masoya ya kamata su fahimci soyayyar gaskiya. Masoyin gaskiya shine kullum ke neman daya ya zama abin alfahari, ya zama nagari. Masoya su zama suna auna junan su a sikeli ta kaifin tunani, su ware kalaman gaskiya dake fitowa daga can karkashin zuciya da kalaman da iyakar su baki. Da dama masoya sun fada tarko a dalilin kalamai na yaudara.


5- BIN IYAYE
Bjjire wa iyaye ba hanya ce ta nuna soyayya ba. Masoyin kwarai shine wanda zai taimaka wa masoyin sa wajen biyayyar iyaye da neman albarkar su.

6- KAUCEWA SHA’AWA
Makauniyar soyayya ke haifar da sha’awa wanda in ba an kai zuciya nesa ba sai an kusanci juna bata karko. Son da zai kai ga sabo batacce ne.Qalilin acikin irin wannan son ne ke kai banten sa, shima sai da kyar auren ke karko da daraja.

7- RAGE SHAKUWA
Shakuwa ga masoya, musamman soyayyar da za’a dau lokaci kafin aure, matsala ce. A baya saurayi kan je zance wajen budurwa duk sati ne koma sati biyu,. A tsawon wannan lokacin da basu tare kowa zuciyar sa ta sami sirki da wani abu na daban. Sabanin yanzu da kullum in da hali sai an hadu kuma in an rabu ba shikenan ba, za’ayi waya, za’ayi chatting da video call, da sauran su. Wadannan duk na kara shakuwa da ta mayar da soyayya makauniya.

8- RAGE KAIFIN SOYAYYA
Abubuwa da dama kan rura wutar soyayya a zuciya ; ya danganta daga wannan mutumin zuwa wancan. Wani wata waka ce daya ji ta tsimin sa na soyayya zai motsa, wani wasu kalamai ne dasu ke rubuce yake karantawa, wani yin kiyamullaili da makauniyar soyayya sai a kiyaye sai lokaci zuwa lokaci.

9- BINCIKE
Duk soyayyar daza a kulla ta ba bincike, da matsala. A dalilin bincike za’a gano illar daza ayi wa soyayya birki tun kafin shakuwa. Sau da dama za’ayi soyayya ta gani a fada amma da anyi aure ba inda abin ke zuwa, sai a rabu sakamakon rashin bincike ne a lokacin. Shi kuwa aure zaman gaskiya ne, makauniyar soyayya batada tasiri ko tayi tasirin boye halin da ba’a so in zama yayi dole sai an fahimta.
10- LITTAFAI DA FINA FINAI
Littattafan soyayya da fina finan da ake kallo, musamman na indiya da kuma namu na hausa, sunyi tasiri kwarai gun dora matasa kan wani bigirevna rashin tabbas. Abinda babu shi sun kirkiro shi, al’umma ta amsa. Wasu abubuwan sun kauce wa al’adar addinin mu da dabi’un mu, bin su kuma ba alkhairi bane. Kwaikwayon salon soyayyar ya jefa masoya a makauniyar soyayya.

Comments

Popular posts from this blog

Sunayen matan manzan Allah /yayansa/sahabbansa

Maganganun hikima 100+ kan soyayya

SOYAYYAR GASKIYA