Sabo mai dadi
CIWO Tayaya zan iya bayyana maka yadda nake ji? Wani zugi ne na ciwo mai tsananin zafi, wani abu ne mai kawar da ido daga ganin komai, ya kore yunwa daga jikina, ya koren jin sautin komai sai nasa, bana ganin komai sai shi. Wai shin mene ne wannan? To ba komai bane face KAI MASOYINA . Hmm! Ina Son Ka. MAFARKI Babu sama da SO daga cikin abubuwan da ke saka ni farin ciki da walwala a rayuwata. Soyayyarka ita ce abun da nake matsanancin so. Rayuwa tare da kai, shi ne mafarkina . Ka amince mu rayu tare, hakan shi ne cikar burina. Ina Son Ka. LOKACI Zan kasance cikin kewarka, ina mai tinanin irin tsawon lokacin da muka kasance tare , cikin so da ƙaunar juna. Fatana a duk inda kake, zaka kasance cikin tina cewa INA SON KA. GIDA Kai ne wanda nake tinani a tsakiyar dare, kuma kai nake fara tinawa da sanyin safiya. Kai ne abun so na a tsawon rayuwa , kuma kai ne wanda nake fatan na rayu tare da shi a gidan Aljanna. Ina matuƙar So da ƙaunarka. LAMBU Tun bayan da na...