Posts

Sabo mai dadi

CIWO Tayaya zan iya bayyana maka yadda nake ji?  Wani zugi ne na ciwo mai tsananin zafi, wani abu ne mai kawar da ido daga ganin komai, ya kore yunwa daga jikina, ya koren jin sautin komai sai nasa, bana ganin komai sai shi. Wai shin mene ne wannan? To ba komai bane face  KAI MASOYINA . Hmm! Ina Son Ka. MAFARKI Babu sama da SO daga cikin abubuwan da ke saka ni farin ciki da walwala a rayuwata. Soyayyarka ita ce abun da nake matsanancin so. Rayuwa tare da kai, shi ne  mafarkina . Ka amince mu rayu tare, hakan shi ne cikar burina. Ina Son Ka. LOKACI Zan kasance cikin kewarka, ina mai tinanin irin tsawon lokacin da muka kasance  tare , cikin so da ƙaunar juna. Fatana a duk inda kake, zaka kasance cikin tina cewa INA SON KA. GIDA Kai ne wanda nake tinani a tsakiyar dare, kuma kai nake fara tinawa da sanyin safiya. Kai ne abun so na a tsawon  rayuwa , kuma kai ne wanda nake fatan na rayu tare da shi a gidan Aljanna. Ina matuƙar So da ƙaunarka. LAMBU Tun bayan da na...

Kaine sirrina

Image
🖌KAINE SIRRI NA🖌 1 Sakamakon jin danayi anyi littafi maisuna “RA’AYINA”yasa na chanza na maidashi “KAINE SIRRI NA”. Ahankali nake tafiya cikin wani babban wuri wanda aka radama suna THE ATTORNEY ‘S WORLD. Office din lawyoyi ne sunfi dari aciki,an kawata su da fulawowi da wasu irin madubai da wutan lantarki masu kyau daban shaawa, koni m shakur na shigo wurin ne Dan neman lawyer dazan bude company a wurin shi. Tafiya na cigaba dayi harna kai gaban wani office sai naji ana hayaniya dariya nadanyi nace nafasa bude kampanin dole na daukoma matsoyana wanga rahoto lol. Bismillahi Rahmanir Raheem. “RA’AYINA ne MUZZAMIL bazan auri wacce batai graduating ba,bazan auri under graduate ha, nafison na auri wacce ta gama school,ta waye, duk inda zan shiga zan iya zuwa da ita batare dajin ko darr araina ba”…da sauri dayan ya tari numfashin shi yace “B maisa kakeda tsatsauran RA’AYI? Kaga niko Kullum burina na auri yar sacandari, wacce zan koyamata komi,soyayya,girmamawa, biyayya, tsorona everything...